ZABEN 2015: Kotu Ta Haramta Yin Anfani da Sojoji Lokacin Zabe

Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya

Daidai lokacin da ake shirin zabe kotunan Najeriya sun daidaitu akan haramta yin anfani da sojoji lokacin zabuka.

Wata kotun daukaka kara a Sokoto kwana kwanan nan ta yanke hukuncin haramta yin anfani da sojoji a wurin da ake hada-hadar yin zabe.

Hukuncin da aka yi a Sokoto yazo daidai da hukuncin da wata kotu ta yanke a birnin Legas a karkashin jagorancin mai shari'a Ibrahim Buba. Alkali Buba Ibrahim yace haram ne sojoji su fito lokacin zabe musamman su kasance inda jama'a ke hada-hadar jefa kuri'unsu. Yin hakan ya sabawa kundun tsarin mulkin kasar da dokokin zabe da kuma alamuran da suka faru can baya a kasar.

Lauya Abdulhamid Muhammad yace kotu tayi nazari da tsarin mulkin Najeriya ne da kuma dokar da ta kafa yin zabe a Najeriya. Haram ne a saki sojoji zuwa wurin zabe ranar da ake yin zaben. Yace dole a ce kotun daukaka kara da ta zauna a Sokoto da wadda ta zauna a Legas duk sun yi bincike mai zurfi kafin su tsayar da hukuncinsu. Sun duba tsarin mulki da dokar da ta tanadi yin zabe.

Batun cewa mutum yayi zabe ya bar runfar zaben ya saba ma dokar zabe. Dokar zabe tace idan an kammala jefa kuri'u jami'an zaben zasu kirga kuri'un kowa na gani kuma su sanarda jama'a sakamakon zaben nan take kowa ya ji ya kuma gani.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Kotu Tana Haramta Yin Anfani da Sojoji Lokacin Zabe - 3' 36"