Haka kuma zaben na zuwa ne a wani yanayi wanda ba a taba ganin irin sa ba a tarihin Niger domin ko ‘yan hamayya sun kaurace masa duk ko da cewa suna da dan takarar dake fatar lashe wannan zabe.
Bayanai sun bayyana cewa an dan samu jinkiri wajen bude runfunar zabe a birnin Yamai sabo da dalilan na rashin maaikata isowa bakin aiki kan lokaci.
Sai dai Shugaban kasa Isoufou Muhammadu da mukarabban sa suka jefa kuriaar su a cibiyar zabe ta daya dake hotel de vil, da musalin karfe 10 na safe.
Ga abinda shugaban ke cewa jim kadan bayan ya jefa nasa kuriaar.
‘’Nayi Zabe lafiya kuma ina fata duka ‘yan Niger su fito dafifi suyi zabe kuma an dauki matakai yadda za a samu ko wane ya fito ya jefa kuriaar sa, ba cikin tashin hankali ko rigima ba ko fadace-fadace ba, abinda nake fata shine cikin wannan zaben duk wanda ALLAH yaba ya kula da hada kanun ‘yan kasa, domi akwai matsaloli da yawa da ‘yan Niger suke fuskanta wadannan matsaloli nayi aiki akan su shekaru 5 amma shekaru 5 ba su isa.’’
Anan Yamai fadar gwamnatin kasar ta Niger ma mutane basu fito ba sosai.
Ga Sule Mummuni Barma da ci gaban Rahoton3’02
Your browser doesn’t support HTML5