Zabe Na Tafiya Kamar Yadda Ya Kamata A Kano Da Jigawa

Ma'aikatan hukumar zabe

A Jihohin Kano da Jigawa An samu isar Jami’ai da kayayyakin zabe da wuri a wasu mazabu na yankunan jihohin.

Rahotanni daga jihohin Kano da Jigawa na nuni da cewa, an fara kada kuri’a a galibin kananan hukumomin dake wajen birnin Kano, amma an samu jinkirin zuwan malaman zabe a kwaryar birni da kewayen Kano, sai dai a jihar Jigawa an bude galibin tashoshin zabe da wuri.

An samu isar Jami’ai da kayayyakin zabe da wuri a wasu mazabu na yankunan jihar Kano kuma galibin masu kada kuri’a sun yi sammako a tashoshin zabe, domin da alama dai an samu sauyin da hukumar zaben Najeriya ta kawo game da yanayin jefa kuri’a na bada sakamako mai kyau, la’akari da cewa, tun da sanyin safiya ne wasu jama’a suka samu sukunin kada kuri’ar su.

To amma an samu jinkiri a kananan hukumomi na cikin birni kamar Nasarawa da Gwale, koda yake akwai irin wannan yanayi a wasu sassan karamar hukumar Tudunwada da Kiru da sauran su, an kai misali karfe 11 na safe babu kayayyakin aiki a babbar tashar zabe ta Kafin Mai Yaki dake karamar hukumar Kiru.

Hon Gambo Saullau shine tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano ya yi tsokaci dangane da wannan yanayi.

A yankin mazabar 'yaryasa ta karamar hukumar Tudunwada kuwa matsasa ne suka kaure da hayaniya lokacin da ake kokarin rarraba kayayyakin zaben da misalin karfe 11 da rabi na rana.

A jihar Jigawa kuwa rahotanni sun nuna zaben na gudana cikin lumana, bayan da kayayyakin da malaman zabe suka isa galibin tashoshin zabe a kan kari.

Mahmud Ibrahim Kwari na dauke da rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Jihohin Kano Da Jigawa A Najeriya