Rahotanni daga hukumomin biyu sun tabbatar da cewa an tanadar da duk abubuwan da suka wajaba domin gudanar da wannan zaben.
Mr. K.K Lubo, shi ne kwamishinan labarai da hulda da jama’a, a hukumar zaben jihar Gombe, ya kuma ce gobe da 8 na safe ya kamata a fara zabe, ana kuma sa ran cewa zai kai har karfe uku na yamma, inda ya bukaci jama’a bayan jefa kuri’a, su koma gida wadanda kuma suke da hakkin tsayawa su tsaya inda ya kamata su tsaya.
Ya kara da cewa kamar yadda jama’a ke ta kira cewa a yi amfani da na'urar tantance katin zabe ta “Card Reader” Mr Lubo, ya ce abinda aka saba amfani da shi a jihar da shi za ayi amfani domin a cewarsa Card Reader ba na Gwamnatin jiha bane na gwamnatin tarayya ne.
DSP Obet Mary, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar ta Gombe, ta ce hukumar a shirye ta ke domin ta tura ‘yan sanda kimanin 7,000 zuwa kananan hukumomi daban daban.
Your browser doesn’t support HTML5