A wata mazaba da Abdulwahab Mohammed wakilin muryar Amurka ya kai ziyara, jami’in zabe ya fara da bayyana wa jama’a dokoki da ka’idodin kada kuri’a da suka hada da fara tantance mutum don gane wadanda suka cancanta su kada kuri’a.
A cewar wani baturen zabe da Abdulwahab ya gana da shi rashin tsari shi ya kawo masu cikas a mazabar, kuma malaman zaben wurin suyi wa dumbin jama’ar wurin kadan shi yasa shirin bai tafi daidai da yadda aka tsara ba, amma wani kuma ya ci sa'a don yace ba a bata lokaci ba wajen tantance shi.
A jihar Gombe kuma, ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton, rahotanni na nuna cewa harkar zaben na gudana babu matsala don tun jiya aka kai kayan zabe a mazabu kuma jama’a sun fito domin kada kuri’a.
Sai dai kuma wani bayani da ba a tantance gaskiyarsa ba, na nuna cewa ‘yan boko haram sun bayyana a wasu kauyuka dake karamar hukumar Nafada kuma sun gargadi jama’a kada su je wurin zabe.
Your browser doesn’t support HTML5