Zabe a Jihar Adamawa

Kamar a wasu jihohi a Najeriya, tun da sanyin safiya mutane suka yi tururuwa zuwa cibiyoyin zabe a jihar Adamawa inda aka fara tantance masu kada kuri’a da suka yi sammako.

Wani malamin zabe da ba’a fadi sunan sa ba ya shaidawa wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz cewa babu wata matsala sosai don mutanen wurin sun basu hadin kai. Game da wadanda na’urar tantance katin zabe ta ki karbar yatsunsu kuma, malamin zaben cewa yayi suna cika masu wani fom wanda hukumar zabe ta tanada.

Alhaji Bamanga Tukur, tsohon shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya, yana daya daga cikin wadanda suka yi sammakon zuwa a tantance su, ya shaida cewa bai taba ganin yadda mutane suka fito kwansu da kwarkwatarsu wajen zabe ba kamar wannan karon.

Mataimakin ‘yar takarar shuban kasa ta jam’iyyar KOWA Sa’idu Bobboi, ya fadi cewa galibin rumfunan zaben jihar sun gudanar da tantance jama’a cikin lumana ko da ya ke ya an sami ‘yar tangarda a wasu wuraren amma suna sa ran komai zai tafi daidai.

Gwamnan jihar ta Adamawa Mr. Bala James Ngilari, na cikin wadanda na’urar tantance katin ta ki daukar hoton yatsun su. A wasu sassan kuma an sami matsalar rashin fara aiki da wuri da kuma rashin isassun kayan aiki.

Your browser doesn’t support HTML5

Zabe a Jihar Adamawa - 3'40"