Yau Talata, Jami’ai da ‘yan sanda a Najeriya suka kiyasta cewa mutane 80 aka kashe tun 31 ga watan Disemba ya zuwa yau, sakamakon tashe tashen hankula tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Mafi yawan tashe tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya akan yin amfani da filaye ne dake yankin middle belt, yankin da ya fi kowane mazauna daga bangarorin kasar dabam dabam.
Kamfanin dilancin labarum Faransa AFP ya ruwaito cewa, Talata shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a kasra yawan yan sanda a jihar Benue
Tashe tashen hankulan manoma da makiyaya makamancin wannan yana cigaba da aukuwa a jihohin dake tsakiyar kasar. Hakan ya sa ake ta samun rabuwar kawauna tsakanin kabilu da addinai, wadda ya janyo kalubale ga alkawarin da shugaba Buhari yayi wa al’ummar kasa a lokacin yakin neman zabe din san a shekarar 2015 akan samun tsaro da kwanciyar hankali.
A watan Nuwambar da ya gabata, an kashe mazauna yankin makiyaya 30 ciki harda yara a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya a saboda wata arangama da aka yi.