Za'a Samarda Makarantu Na Kusa Domin Mata

Gwamnatin jamhuriyar Nejar, tayi alkawarin biyar malaman makaratar kasa duk abinda suke bin gwamnatin,ta kuma jaddada alkawarinta na baiwa yara ilimi kyauta daga matakin firamari har zuwa sakadare.

Ministan Ilimi, na tsakiya na kasar Malam Sani Abdulrahaman, ne ya bada wanna tabbacin hakkan a shirin muryar Amurka, nay au da gobe.

Ministan yace gwamnati na kokari samar da makaratun sakandare na kusa saboda mafi yawan iyaye basu yadda ‘ya’yansu mata su tafi Makaranta, nesa.

Ya kara da cewa samarda makaratun sakandare na kusa zai karfafawa iyaye guiwar sa ‘ya’ya mata a makaranta. Ya kuma ciu gaba da cewa akwai tallafi da gwamnati take baiwa ‘ya’yan masu karamin kafi domin tabbatar da cewa sun samu ilimi.

Irin wannan tallafi da gwamnati take baiwa mata, yana kara masu karfin guiwar yin karatun, kuma hukumomi na zagayawa makarantun domin ziyartan daliban da ganin irin yadda karatun ke tafiya.

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Samarda Makarantu Na Kusa Domin Mata - 6'23"