Kakakin majalisar dokokin Zimbabwe Jacob Mudenda, ya ce za'a rantsar da Emmerson Mnangagwa, a zaman shugaban kasar ranar Jumma'a, biyo bayan murabus na Robert Mugabe, mutumin da ya juma yana mulkin kasar,al'amari da ya auku jiya talata.
Sanarwar da kakakin majalisar ya bayar a yau Laraba, tana zuwa ne a dai dai lokacinda Mnangagwa yake shirin komawas kasar. Haka kwatsam tsohon mataimakin shugaban ya gudu daga kasar a ranar shida ga watan nan, bayan da Mugabe ya kore shi daga kan mukaminsa.
Masu motoci sun yi ta busa kahon motocin su yayinda 'yan kasar suke ta raye raye, da masu rangwada a Harare, babban birnin kasar don murnar murabsu din Mugabe, da ya bayyana jiya Talata, a cikin wasikar da kakakin majalisar Mudenda ya karanta a zauren majalisar.