Tashar ta farko za'a ginata ne a garin Obollo-Afor dake jihar Enugu, inda tuni aka samu katafaren fili mai tsawon kadada 16, kuma zata dauki dukkan manyan motoci da kan tsaya a garuruwan dake kan manyan hanyoyin da hakan kan haddasa cunkoso da ma hatsari,.
Wakili a hukumar kula da wadannan tashoshi Injiniya K.C. Izuwah yace ya kamata gwamnatin Nigeria ta kafa duka a zata tilasta direbobi su rika tsayawa don hutawa; don an gano yawancin direbobin kan yi barcin sa’a 4 ne kacal cikin sa’o’I 24 inji Injiniya Chidi K.C. Izuwah.
Ya ci gaba da cewa akwai bukatar samar da tashoshin madakatar manyan motocin domin direbobi su samu su huta a kuma kaucewa hadarin da kan faru a kan hanyoyi sanadiyar ajiye manyan motocin a gefen tituna
Izuwah ya ce tashoshin na zamani za su zama da masaukan baki,gidajen abinci, bankuna, asibitoci, kotuna, wuraren ibada, makanikai har ma da wajen shakatawa da wanke motoci.
Shugaban hukumar zirga-zirgar harkar kasuwanci ta jiragen ruwa Hassan Bello, ya ce za a fara aikin nan take kuma za a kafa irin tashoshin a duk garuruwan da manyan motoci ke tsayawa, baya ga rage hatsaari, zai kuma bunkasa tattalin arzikin al’ummar yankunan.
Kungiyar direbobi da ake kira NURTW a takaice data masu manyan motocin sufuri wacce ake kira NARTO a takaice, sun amince da shiga wannan tsari don inganta rayuwar direbobin da kula da lafiyar motocin.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5