Za'a Daina Samun Mutuwar Mata A Yayin Haihuwa

Wa 'yansu mata masu shirin haihuwa

Akwai bukatar gwamnatoci a kowane mataki su kara kaimi wajen ilmantar da mata Ungozoma, hanyoyin karbar haihuwa na zamani.

A tabakin wata kwararriya a fannin lafiya Dr. Hauwa Abdullahi, ta asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ta yi nuni da cewar tunda mafi akasarin mata sun fi aminta da wadannan ungozoman, to lallai akwai bukatar a ilmantar dasu, su san wasu hanyoyi da yakamata su dinga taimakama mata wajen samun saukin haihuwa da kuma suma yaran da ake haifa su samu nagartacciyar lafiya.

Lallai yakamata a samar da wani tsari na horas da wadannan ungozomomi a kowane mataki, suna bukatar horaswa na yaki da jahilici da kuma sanin mai duniya take ciki a bangaren lafiya.

Domin ta yin haka ne kawai za’a iya samun rage yawan mace mace na mata masu juna biyu da nakuda a lokacin haihuwa.

Mafi akasarin wadannan ungozoman basu da wani horaswa, amma saboda dadewa da sukayi suna wannan aikin za'a ga cewar suna da kwarewa da takamata a wajen taimakawa. Yakamata gwamnatoci da masu ruwa da tsaki a harkar lafiya su basu kwarin gwiwa a wannan bangaren.