Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta yanke shawarar kawo karshen amfani da gidajen Yari masu zaman kansu, bayan da aka tabbatar da cewa basu da tsaro da inganci irin na gwamnatin tarayya.
WASHINGTON D.C —
A wata sanarwa da aka fitar jiya Alhamis, mataimakin shugaban ma’aikatar Sally Yates, ya rubuta cewa gidajen Yari masu zaman kansu basa aiki kamar yadda na gwamnati suke, kuma basu da wasu shirye shirye masu amfani,” haka kuma suna cin kudi sosai, basa bayar da tsaron da ya kamata.
Yates yace “bukatarmu itace mu rage amfani da ire iren gidajen Yarin har zuwa lokacin da zamu daina baki ‘daya.”
Sanarwar tace kaso 15 cikin 100 na fursunonin Amurka, suna gidajen Yarin masu zaman kansu.