Za'a Ci Gaba Da Biyawa Dalibai Kudin Jarabawar WAEC

Gwamnatin jihar Borno, tace zata ci gaba da biyan kudaden jarabawa na dalibai da zasu kammala karatun karshe wanda aka dakatar tsawon shekaru biyu Kenan sakamakon rufe makarantu da aka yi a jihar.

An dai rufe makarantun sakadaren dake fadin jihar ne tun lokacin da ‘yan kungiyar Boko Haram, suka yi awon gaba da daliban makarantar mata na garin Chibok.

Gwamnatin jihar ta bada wannan tabbaci ne a lokacin da Kwamishinan ilimi na jihar Borno, Musa Inuwa, ya ziyarci wasu makarantun da aka sake budewa a cikin garin Maduguri.

Ya kuma kara da sharadin cewa za’a yi masu wani jarabawa na gwaji kuma sai wanda ya ci wannan jarabawa ne sannan za’a bashi damar rubuta jarabawar kashen kafin Gwamnatin jihar ta biya masa irin wannan kudin.

Your browser doesn’t support HTML5

Za'a Ci Gaba Da Biyawa Dalibai Kudin Jarabawar WAEC - 3'43"