Za Mu Ma Ku Aiki, Amma Ba Za Mu Ba Ku Kudin Jama'a Ba - in ji A'isha Buhari

  • Ibrahim Garba

A'isha-Buhari.

Hajiya A'isha Buhari, matar Shugaban Najeriya mai jiran gado, ta ce duk mai tunanin wai za su rika kwasar kudaden gwamnati su na kyauta to su canza tunani

Matar Shugaban Najeriya mai jiran gado A’ishatu Buhari ta yi gargadi ga masu zuwa wurin ‘yan siyasa musamman ma gidan gwamnatin jiha ko fadar Shugaban kasa a ba su kudi da su kwana da sanin cewa ita fa ba za ta bai wa wani kudi ba saboda ko ita ma ba ta gan su ba.

A wani bayanin da ta yi mai kama da shagube kan yadda ake almubarranci da dukiyar al’umma a maimakon a yi amfani da kudin jama’a a samar masu da ingantattun matakan tsaro da magunguna da imili da sauransu, Hajiya A’isaha Buhari ta ce su burinsu shi ne su tabbatar da cewa kowa ya kwanta cikin kwanciyar hankali ba tare da ya wayi gari babu ‘ya’ya wasu miyagu sun sace su ko kuma an sace mace an bar ta da ‘ya’yanta; ko kuma an yanka mutum an bar matarsa da ‘ya’ya ba uba ba.

Ita kuwa tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan jihar Filato Madam Pauline Tallen ta ce sabanin yadda wasu miyagun kuma su ka yi ta hasashe, batutuwan addini da kabilanci da bangaranci ba su yi wani tasiri ba. Ta kuma kara da cewa Janar Buhari zai ba da kunya ga masu cewa zai nuna banbancin addini ko kabila. Ita ko madam Binta Mercy Garba zababbiyar ‘yar Majalisar Dattawa mai wakiltar arewacin Adamawa, ta ce ko da ma an shafe ofishin matar shugaban kasa, A’isha Buhari za ta iya daukaka muradun mata a matsayinta na matar Shugaban kasa mai sauraron kowa ko kuma ta bi ta Ma’aikatar Mata ko ta Ilimi da dai sauransu .

Your browser doesn’t support HTML5

A'isha Buhari: Za Mu Ma Ku Aiki, Ba Za Mu Ba Ku Kudin Jama'a Ba 3'12"