"Za Mu Garzaya Kotu Akan Sakamakon Zaben Da Aka Yi" - PDP

Babban Taron Jam'iyyar PDP Na Kasa

A cikin makon da ya gabata ne aka yi zabukkan gwamnoni a jihohin Bayelsa da Kogi da ke Najeriya, inda a jihar Kogi gwamna Yahaya Bello ya sake komawa kujerarsa, a Bayelsa kuwa David Lyon ne ya yi nasara.

Sai dai da alama dukda an gama gudanar da zabukkan, jam'iyyar PDP wacce 'yan takaranta biyu duk basu yi nasara ba, ta ke neman kalubalantar sakamakon zaben.

Jam'iyyar ta bayyana cewa ba ta amince da sakamakon zaben da aka yi a dukannin Jihohin biyu ba, saboda haka ta yi alkawarin garzayawa kotu.

Mai magana da yawun Jam'iyyar, Kola Ologbondiyan shi ne yayi suka da kakkausar murya, inda ya ce Jamiyyar ba ta amince da sakamakon zaben Gwamnonin da a ka a yi a Jihohin Bayelsa da Kogi ba.

A Bayelsa dai mutane na ganin cewa PDP tana neman a share mata hawaye ne kawai, saboda rasa Jihar da ta yi a yanzu, bayan shafe kusan shekara 20 tana mulkinta.

Babban jigo Mr. Sunny Monidafe na Jamiyyar APC, ya ce a ganinsa ba laifin APC bane cewar PDP bata ci zabe ba.

Kalaman nasa sun samu goyon bayan Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson wanda yake kammala wa'adinsa karo na biyu.

Bayan wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa ba'a gudanar da zabbukan yanda ya kamata ba, shugaban Cibiyar Inganta Damokradiya da cigaban kasa, Farfesa Jibo Ibrahim, shima ya tofa albarkacin bakinsa inda yace "wadannan koke-koke da ake samu ba za su kawo wa demokradiyar kasa cigaba ba."

Ga karin bayani daga wakiliyarmu Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

"Za Mu Garzaya Kotu Akan Sakamakon Zaben Da Aka Yi" - PDP 3'10"