Za a Yi Wani Nazari Kan Rufe Iyakokin Najeriya

Kasashe 15 na Afirka ta Yamma za su yi wani nazari kan irin tasiri ko illar da kasashen su ke fuskanta sakamakon rufe kan iyakokin Najeriya tun watan Agustan shekarar da ta gabata.

Najeriya dai ta rufe kan iyakarta ne don yaki da fasa kwabri, matakin da daga bisani ya shafi sauran kayan masarufi da kuma manufar hana shigo da makamai.

Sanarwa kan nazarin da za a yi, ba ta fadi takamaimai lokacin fito da rahoto kan batun ba, amma Ministan Harkokin Kasashen Waje na Najeriya, Goefrey Onyeama, ya ce za a yi hakan nan ba da dadewa ba.

A bayaninsa game da makasudin rufe iyakar ga manema labarai, Onyeama ya ce ya zama wajibi a kula da ingancin kayan da ke ratsa kan iyakar Najeriya.

"Za a tabbatar da cewa kayan da ke shigowa an kera su, ko samar da su a cikin kasashen Afirka ta Yamma kuma a tabbatar duk hajar da za ta shigo daga waje da yankin an sanya ma ta fiye da harajin kashi 50 ciki 100," a cewar Goefrey Onyeama.

Sai dai wani dalilin na rufe iyakar shi ne yunkurin sanya Najeriya ta zama wata babbar cibiyar kasauwanci a Afirka.

Wasu jami’an tsaron Najeriya sun bayyana amfanin ci gaba da rufe iyakar har sai an samu nasarar da ake bukata ta hana makamai shiga hannun ‘yan ta’adda.

Wasu matakan da hukumar hana fasa kwabri ta dauka na hana sauke mai a tazarar kilomita 20 daga kan iyaka, bai yi wa wasu ‘yan majalisar wakilai na yankin kan iyakar dadi ba.

Dan majalisar wakilai daga jihar Katsina, Sada Soli jibiya, ya ce illar matakin zai kare ne kan talakawan yankin, maimakon ya zama maganin fasa kwabri.

Shugaba Buhari ya nuna alamun in dai aka bi ka’idar hada hadar kasuwanci ta yankin, gwamnatin sa za ta bude iyakar.

A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Za a Yi Wani Nazari Kan Rufe Iyakokin Najeriya