Za a Yi Wa 'Yan Takara Gwajin Miyagun Kwayoyi a Jihar Kano

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA zata gudanar da gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi da ababen sanya maye akan dukkanin ‘yan takarar shugabancin karamar hukuma da kansiloli a kananan hukumomin jihar Kano 44

Yanzu haka dai hukumar zaben ta Kano ta ce ta shigar da wannan batu a jerin sharrudan tsayawa zabe a wannan zabe da zata gudanar. Bisa ga cewar shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka, doka ta basu ikon gindaya sharuddan tsayawa takara, wannan kuma na daga cikin sharudan da suka jera. Bisa ga cewarshi, kamata ya yi jam’iyu su tantance ‘yan takararsu su kuma tabbata basu shan miyagun kwayoyi kafin su tsayar da su takara. Ya ce za su bukaci shaidar cewa dan takara ba ya ta’amali da miyagun kwayoyi daga hukumar NDLEA kafin su bashi takardar tsayawa takara.

Matsayin ‘yan takara

Ya zuwa yanzu dai masu neman takara sun fara bayyana aniyar su ta biyayya ga wannan sabon tsari. Sai dai sun bukaci a bi wannan tsarin bai daya. Sun bukaci a gwada ‘yan takarar da jam’iyar su ke mulki da wadda ba ta mulki, ba wai a gudanar da gwajin kan ‘yan takarar jam’iyun hamayya kadai ba domin dukansu jama’a za su yi wa aiki. Banda haka kuma, sun bukaci a fitar da sakamakon binciken a bainin jama’a domin kowa ya san wanda ya ke shan kwaya da wanda ba ya sha, domin kada wadansu su shafawa wadansu kashin kaza.

Abinda ya sa ake gwajin

Hukumar ta bayyana cewa ana yin irin wannan gwajin ne domin tabbatar samun shugabanni na kwarai da zasu rike amana

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, kwamandan hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin ababen sanya maye a jihar Kano Dr Ibrahim Abdul ya bayyana cewa, ba wannan ba ne karon farko da ake gudanar da irin wannan gwajin kan wadanda zasu rike mukaman shugabanci.

Bisa ga cewar shi, an yi irin wannan gwajin a lokutan baya kan wadanda aka nemi ba mukaman zaunannun sakatarori da aka fi sani da famanant sakatare, aka kuma tarar wadansu na dauke da kwaya a jikinsu. Banda haka kuma, a lokutan baya ana yin irin wannnan gwaji a fadar Mai martaba Sarkin Kano inda ake yiwa dakatai, da masu uguwa da sauran masu rike mukaman sarauta gwaji.

Kwamandan ya bayyana cewa, an sami wadanda aka yi niyar ba mukamai da dama da na’uin kwaya iri iri a fitsarinsu bayan gwaji, wadanda da bakinsu sukan fadi irin kwayar da suke sha. Ya ce an sire sunayen mutane da dama daga jerin wadanda za a ba mukaman siyasa sakamakon samunsu da kwaya a fitsarinsu.

Menene doka ta tanada?

Tuni dai kwararru akan lamuran ta’ammali da miyagun kwayoyi da ababen sanya maye ke cewa, matakin hukumar ta NDLEA zai tasiri ga tsarin samar da shugabanni domin zai sa masu neman mukaman siyasa su yi nemi kare mutuncinsu tsakanin al’umma.

Amma a nasu bangaren ‘yan siyasa na cewa, ko da yake yunkurin yana da kyau, amma akwai kalubale domin bisa ga cewarsu, gwada jinin ‘yan siyasa da jami’an gwamnati ba zai hana su gudanar da ayyukansu na son zuciya ba.

Sai dai kwararru a fannin shari’a sun ce ba zai yiwu a aiwatar da wannan tsarin ba a halin yanzu domin ya sabawa doka. Bisa ga cewar Dr Nasiru Adamu Aliyu lauya mai zaman kansa a Kano tilas sai majalisar dokokin Kano tayi garanbawul ga dokar zabe ta jihar kafin a iya aiwatar da wannan tsarin.

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da wannan yunkurin hadin gwiwa tsakanin hukumar zabe ta jihar Kano da hukumar dake yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi ta Najeriya na gudanar da gwajin ababen sanya maye akan dukkanin ‘yan takarar da zasu shiga zaben kananan hukumomi da hukumar zaben ta Kano zata gudanar a cikin watan Janairun badi.

A ranar 16 ga watan Janairun badi ne hukumar zaben jihar Kano zata gudanar da zaben kanananan hukumomi a jihar ta Kano, inda za’a zabi sabbin shugabannin hukumomi 44 da kansiloli 484 a fadin jihar ta Kano.

Abin jira a gani dai shine ko za’a mika kudirin gyran dokar zabe ga zauren majalisar dokokin Kano kafin ranar 16 watan Janairun badi ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

: Za a Yi Wa Yan Takara Gwajin Miyagun Kwayoyi-3:00"