Za A Tabbatar Da Gina Jami’ar Assalam - Aminu Dantata

Sharerren dan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya jagoranci gagarumin taron kaddamar da kwamitin kafa jami’ar Assalam ta Jibwis a masarautar Hadejia jihar Jigawa kan kadada 150.

Alhaji Aminu Dantata ya ce da yardar Allah za a tabbatar da gina jami’ar.

Wannan taro na zuwa daidai lokacin da jami’o’I masu zaman kan su ke kara samun tagomashi a Najeriya don samar da damar guraben karatu ga dinbin dalibai da su ka cancanci shiga ajin karatun matakin “A”.

Farfesa Umar Labdo wanda ya taba zama shugaban jami’ar Alkalam ta Katsina, shi ne shugaban kwamitin.

Shi kuma Farfesa Aliyu Bunza na jami’ar Usman Fodio ya ce Kafa irin wadannan jami’o’I ya zama abu mai muhimmnacin gaske a wannan lokaci na bunkasar kimiyya da fasaha.

Shugaban Jibwis Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce duk daliban da su ka cancanta za su iya shiga jami’ar da zarar ta fara aiki.

Gwamnatin jihar Jigawa da mai martaba Sarkin Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje sune suka ba da gudunmawar makeken filin.

Ga karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Za A Tabbatar Da Gina Jami’ar Assalam - Aminu Dantata