Za A Samu Jinkiri Wajen Kafa Gwamnatin Farar Hula A Sudan

Sudanese protesters and wave flags during a rally at the Green Square in Khartoum, Sudan, July 18, 2019.

Hanyar da kasar Sudan za ta iya bi don kafa gwamnatin farar hula za ta zama mai tsawo da wahala, a cewar babban manzon Amurka a kasar, mako guda bayan da majalisar mulkin sojojin kasar da kungiyoyn ‘yan adawa suka cimma yarjejeniya da ta bayyana yadda za a gudanar da mulki cikin shekaru uku.

Yarjejeniyar dai ta biyo bayan zanga-zangar siyasa da ta shafe watanni bakwai, ta kuma saukar da dadadden shugaban kasar Omar al-Bashir, kuma yawancin zaman tattaunawar ya hada da kusoshi a kasar da ke da arzikin mai.

Amma akwai sauran ayyuka masu yawa da su ka rage a yi, a cewar Donald Booth, jakadan Amurka na musamman a Sudan. Tun lokacin da aka nada shi a matsayin makonni shida da suka gabata, Booth ya shirya zaman tattaunawa masu yawa a Khartoum da Brussel da kuma Addis Ababa, inda bangarori daban-daban ke kokarin bayyana damuwarsu da kuma yadda suke kallon sabuwar kasar Sudan zata kasance.

A wani taro da aka gudanar ta kan waya a Brusels jiya Talata, Booth ya yi nuni ga wasu bangarorin da ya kamata a tattauna akansu.