Pompeo ya gayawa manema labarai jiya Lahadi cewa , wannan ya shafi yaddda al'ummar kasar Iran bata jin dadin gwamnatinta kuma shugaba Trump ya fayyace haka karara. Muna son alummar Iran su kasance sun da murya mai karfi kan wanda zai zama shugaban su.
Ya ce fadar White House zata bada cikakken bayani yau Litinin nan kan takunkumin da za'a sanya wanda kuma zai fara aiki gobe Talata kan kamfaninnikan Iran, da suka hada da kamafonin kera motoci, gwal, kwal da karafu.
Ya kara da cewa, ba za'a bar Iran ta kara sayan jiragen Amurka ko na igila ba. An kuma ba daidaikun al'umma da kuma harkokin kasuwanfci dake hulda da wadannan kamfanonin wa'adin kwanaki casa'in su dakatar da ayyukan su. Yau litinin Wa'adin ya cika.
Iran ta sha musunta cewa tana gudanar da ayyukan nukiliyarta da nufin kera makaman nukiliya .