Bayan cikar wa’adin kwanaki 40 na kama shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ba tare da hukumar sojin Najeriya ta yi nasarar kama shi, kamar yadda Babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Yusuf Burutai ya umurta ba, hukumar sojin ta ce dama wa’adin wani jadawali ne na tayar da azamar kama Shekau, saboda haka rashin kama Shekau cikin wa’adin da aka gindaya ba ya nufin shikenan an kawo karshen kama Shekau. Ta ce za a sabunta wannan wa’adin a kuma cigaba da kokarin kama Shekau.
Babban kwamandan rundunar “Operation Lafiya Dole” mai yaki da Boko Haram, wanda ya yi karin bayani, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya ce a yanzu an sa batun kama Shekau na kan gaba. To amma wani tsohon hafsa a hukumar leken asirin Najeriya, Aliko Arrashid Harun y ace dama bai kamata a rika bayyana matakin soja mai sarkakkiya ba sai bayan an aiwatar kafin a rika cewa dama an shirya yin hakan ne.
Tsohon jami’in tsaron y aba da misali da yadda Amurka kan sakaya muhimman sojan da ta ke daukawa har sai ta yi nasara kafin ta kuma shiga bayanin cewa dama ta tsara hakan ne. Ya ce Amurka ta shafe shekaru shida ta na kokarin kama marigayi Usama bin Ladan ba tare da gaya ma duniya ddabarunta na kamawa ko kashe Bin Ladan ba.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5