Za a Kai Kofin Gasar Kwallon Kafar Mata Ta Duniya Birnin Tarayyar Abuja

A ranar sha daya ga watan Afrilun wannan shekara ce za kawo kofin gasar kwallon kafar mata ta duniya a birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda Najeriya ta zama kasar farko a cikin kasashe 24 da za a zaga da kofin, kafin fara gasar ta wannan shekarar 2019 a kasar Farnsa.

A cewar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, shahararrun ‘yan wasa kamar Kristine Lilly da Laura Georges sune ke dauke da kofin a birnin Paris inda aka dauko kofin za a zaga da shi, kuma nan ne za a yi wasan farko na gasar cin kofin a cikin watan Yuni.

Da farko za a kai kofin ne a kasar Jamaica kafin a zaga da shi a kasashen 24 da zasu shiga wannan gasar ta nahiyoyin duniya guda shida da zummar baiwa masu sha’awar wasa damar ganin kofin a kusa da su.

Kasashen da zasu shiga gasar kuma za a kai wannan kofin sun hada ne da Chile, da Argentina, da Brazil, da Amurka, da Jamhuriyar Korea, da Japan, da China, da Thailand, da Australia, da New Zealand, da Sweden, da Afrika ta Kudu, da Kamaru da kuma Najeriya kanta da sauran su.

Kungiyar kwallon kafar matan Najeriya ta Falcons tana cikin kungiyoyin bakwai da suka samun damar shiga kowace gasar cin kofin duniya kuma Falcons ta mata kana tana cikin rukuni A tare da Faransa mai masaukin baki da Norway wacce ta ci gasar a shekarar 1995 da kuma Jamhuriyar Korea.

Najeriya dai ta shiga kowace gasar cin kofin duniya tun lokacin da aka kirkiro ta a shekarar 1991, amma dai har yanzu bata taba daukar kofin ba.