Za A Karya Farashin Sabuwar Wayar Samsung Galaxy Fold 2

Galaxy Fold

Rahotannin baya-baya da sun nuna cewa farashin sabuwar wayar kamfanin Samsung ta Galaxy Fold 2 mai budewa zai ragu.

Za a fara sayar da ita daga dalar Amurka $1,980 kwatankwacin naira N700,000.

Sabuwar Wayar Samsung mai Budewa da kullewa

Wayar dai ta kasance cikin jerin wayoyi mafiya tsada a fadin duniya, duk da cewar tana da tsari irin na wayoyin da aka daina amfani da su.

Amma wasu rahotannin da suka fito daga kasar Koriya ta Kudu na cewa, kudin wayar zai sauka kamar ragon Malam.

Idan kuwa hakan ya tabbata, akwai labari mai dadi ga masu sha’awar sayen wannan wayar, domin kuwa an kiyasta kudin wayar na iya komawa kimanin dalar Amurka $860 kwatankwacin naira N300,000.

Sabuwar wayar Samsung

Wayar dai an inganta ta da kyamarori guda 6, haka ana sa ran kamfanin na Samsung ya fitar da sabuwar wayar ta Galaxy Bloom ko Galaxy Z Flip, daga ranar 11 ga watan Fabrairun wannan shekarar don masu bukata a kasuwannin duniya.