Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Prof Yemi Osinbajo yace nan bada jimawa gwamnatin tarayya zata tabbatar da aiwata kafa hukumar raya yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Prof Osinbajo, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci jihar Borno domin kaddamar da wasu ayyuka a karkashin shugabancin gwamnar jihar Kashim Shettima wanda suka hada da makaratu, hanyoyin titi da wasu rukunan gidajen marayu.
Mataimakin Shugaban kasar yace gwamnan jihar Borno Kashin Shettima ya yi ayyukan yabawa , mussaman ma wajen ganin an samar da dawwamaman zaman lafiya a jihar.
Ya kara da cewa “ Mutanen da ke aiki dani a anan yanzu zasu iya bada shaidar yadda gwamnan ya dauki matsalar a wuyansa, don ganin samun zaman lafiya a jihar," kuma yace "muna so mu tabbatar maku cewa batun kafa hukumar raya yankin arewa maso gabashin Najeriya, shine a gaban gwamnatin tarraya wanda a yanzu haka Shugaban kasa ya rattaba hannun akai kuma hakan zai bamu damar sake gina wannan jihar dama sauran wasu jihohi da wannan iftila’e ya shafa”
Shima Gwamnar Jihar Borno Kashim Shettima, yace “Mataimakin Shugaban kasar na kishin mutanen jihar Borno, ya kara da cewa Mataimakin shugaban kasa Pasto ne kuma kirista ne daga kudu masu yammacin Najieriya wanda ya bigi kirji ya gina makarantar marayun musulimai na boko haram wanda ta kasance makaranta maki kyau a Najeriya”
Mai Martaba Shehun Borno Dr Alhaji Abubakar Garba Ibn Al-kanemi ya ce akwai bukatar gwamnatin tarraya taba mutanen Borno dama ta mussaman . Mussaman wajen dibar ma’aikata da suka shafi jami’an tsaro kamar sojoji da 'yan sanda, da ma’aikatan gidan yari, ganin yadda da dama irin wadannan ma’aikatan sun rasa rayukan su a jihar sakamakon rikicin Boko Haram.
Ga wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu, da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5