ABUJA, NIGERIA -Ministan na harkokin cikin gida ya tabbatar da cewa, 'yan Najeriya zasu rika samun fasfo dinsu ta manhajar yi da kanka wato "Online." Ya kuma ce wannan sabon tsari na samun fasfo zai fara aiki ne daga ranar 8 ga wannan watan na Junairu.
Ministan ya kara da cewa, ‘yan Najeriya da kansu zasu cike guraben da suka tanadar a manhajar, wanda zai basu damar samun fasfo ba tare da sa hannun wani ma'aikaci ba.
Tunji-Ojo, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ziyarar aiki a babban ofishin masu duba shige da fice dake birnin Abuja.
Ministan, ya kara da cewa, tuni suka fara gwajin fara amfani da wannan sabon tsarin samar da fasfo, kuma zasu kaddamar da shi kai tsaye kamar yadda aka tanadar.
Kazalika, Ministan ya ce wannan tsare-tsaren yana daga cikin muradun Shugaba Tinubu na cimma sabuwar manufa, kuma hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da kuma gano fasfon bogi domin gwamnati ta tanaji ma'aikata da za su kasance a dukkanin kananan hukumomin kasar domin tantance sahihancin takardun neman fasfo.
A hirarsa da Muryar Amurka, Rilwanu Ladan mai sharhi akan lamuran da suka shafi harkokin yau da kullum, ya ce "wannan sabon tsari na samun fasfo zai taimaka wajen rage cin hanci da ake zargin wasu ma'aikatan hukumar bada fasfo ke yi, kuma hakan zai takaita bata lokaci wajen samun fasfon, sai dai wannan sabon tsarin yana dauke da kalubalai da dama da suka hada da inganci lambar ‘dan kasa ta NIN da kuma intanet, wanda zasu iya kawo tsaiko”
Yanzu sai dai a jira aga yadda wannan shirin zai amfani ‘yan kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:
Your browser doesn’t support HTML5