Za'a Kada Kuri'a Don Zaben Kasar Da Zata Karbi Bakoncin Gasar CAF

Bayan da hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Nahiyar Afrika (CAF) ta karbe damar gudanar da gasar cin kofin Nahiyar kasashen Afrika na 2019, a hanun Kamaru saboda rashin kammala shirye shiyen kayan aiki da kuma tsaro.

Shugaban hukumar ta CAF, Ahmad Ahmad, ya ce a ranar 14 ga watan Disambar da muke ciki, 2018 za’a rufe karbar takardun bukatar neman karbar bakuncin gasar daga kasashen dake nema, haka kuma a ranar 25 ga
watan Disamban CAF za ta tantance kasar da ta cancanta na samun damar karban bakuncin gasar ta 2019.

Inda hukumar ta Nahiyar Afrika CAF, ta bayyana cewar ranar 9 ga watan Janairu, 2019 a matsayin ranar da za ta bayyana sunan kasar da za’a
baiwa damar karbar bakuncin gasar cin kofin Nahiyar ta Afrika.

Sai dai kasar ta Kamaru da aka karba a hannunta za ta karbi bakuncin gasar
a shekara ta 2021. Wannan gasar cin kofin ta Nahiyar Afrika ta 2019 za a bude shi ne a ranar 15 ga watan Yuni a kuma kammala ranar 13 ga watan Yuli shekarar.

Kasashen Afrika da dama sun nuna sha'awar su na karban wannan bakuncin gasar, inda wasu ke ganin kasar Morocco ta fi cancanta ta dauka nauyin gasar.