Za A Hukunta Sojoji Masu Hannu A Magudin Zabukan Ekiti da Osun Da Na Kasa Na 2015

  • Ibrahim Garba

Laftana-JanarTukur Yusuf Burata

Yayin da bangarori daban-daban a Najeriya ke kokarin inganta kansu, su ma sojojin Najeriya sun tashi haikan wajen kare mutuncinsu. Na baya-bayan nan shi ne yakin da su ka kuduri aniyar yi da masu magudin zabe.

A wani al’amari mai kama da wanzuwar yaki da rashin gaskiya, rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin zakulo duk wani sojan da ya taka rawa a duk wani magudin zaben da aka aikata a Ekiti ko Osun ko ma kasar baki daya. Hasalima, hukumar bincike ta mika rahotonta ga Babban Hafsan Sojin Kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Burutai.

Da ya ke mika rahoton, Shugaban Hukumar Binciken, wanda shi kuma ne Babban Kwamandan Runduna Ta Daya Ta Sojin Najeriya, Manjo-Janar Adeniyi Oyibade ya ce daga cikin shawarar da kwamitin binciken ya bayar har dayin ritaya ma wasu sojojin ba tare da bata lokaci ba, a rage ma wasu matsayi a kuma a gurfanar da guda gaban kotu saboda zargin karbar nagoro.

Cikin sojojin da abin ya shafa har da wadanda za a cigaba da sa ido kan take-takensu, da wadanda kuma Hukumar EFCC za ta karasa bincike kansu. Akwai kuma wasu kimanin 60 daga masu mukamin manjo-manjo zuwa kasa da za a ba su takardar gargadi.

Ga dai wakilinmu a Abuja, Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Za A Hukunta Sojoji Masu Hannu A Magudin Zaben Ekiti, Osun da Na Kasa Na 2015 - 2'00''