Hukumar da ke kula da filayen jiragen sama a Najeriya, FAAN ta fitar da sharuda gabanin bude filayen jiragen da suka jima a garkame a kokarin takaita yaduwar cutar coronavirus.
A cikin sharudan da hukumar ta gindaya, akwai hana wadanda ba tafiya zasu yi ba shiga aihinin ginin filayen jiragen.
FAAN ta kuma ce ana bukatar duk matafiya da su isa filayen jiragen sa'o'i uku kafin lokacin tafiyar domin a Iya gudanar da bincike dangane da cutar Covid-19 kansu.
Wadanda suka zo daukar matafiyan da suka dawo suma za a hana su fitowa daga motocinsu, har sai wadanda suka zo dauka sun fito daga ginin filayen jiragen.
FAAN ta bayyana wadannan sharudan ne a shafinta na Twitter.
Duk da dai gwamnatin ba ta bayar da ainihin ranar da za a bude filayen ba, ana sa ran cewa ranar 21 ga wannan watan na Yuni za a yanke hukuncin yaushe za a bude su.
Tun watan Maris din da ta gabata ne aka rufe filayen jiragen domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.