Za A Fara Sayar Da Motocin Da Aka Kera A Najeriya Kwanan nan

Shugaban hukumar kera ababen hawa a Najeriya Jelani Aliyu, ya ce nan da wattani 3 masu zuwa, za a fara sayar da Motocin da aka kera a gida Najeriya akan kudi kalilan.

Jelani Aliyu ya ce a cikin shekaru biyu da ya karbi shugabancin hukumar ya sami nasarar shiga yarjejeniya da sanannun kamfanonin kera motoci na duniya irin su Honda, Innoson, da kamfanin Dangote, da Aston, da kuma Anamco, wadanda tuni har sun fara kera motoci a Najeriya.

Jelani ya ceza a sayar da motocin ga 'yan Najeriya a farashe mai rahusa, domin mai son mota zai biya kashi 10 kacal na kudin motar sai ya tafi da motar sannan ya cika kudin cikin shekaru biyar.

Jelani ya ce akwai tanadi na musamman da aka yi na wuraren gyaran motoci wadanda kwararru ke aiki a wurin, kuma za su yi gyaran motocin yadda ya kamata.

'Yan Najeriya irin su tsohon dan majalisar aakilai, Umar Faruk Abdullahi, Maji-kiran Gwandu, ya bayyana jin dadin sa akan wannan ci gaba da aka samu inda ya ce dama Najeriya kasa ce da Allah y ake son ta a soboda haka yayi mata ma'adinai iri daban daban da mutane masu basira da kwazo kamar irin wannan na kera motoci.

Ita ma Madam Rona Alkyaban Tula ta ce abin farin ciki ne abin alfahari ne, idan har Najeriya za ta shiga cikin ayarin kasashen da ke kera motoci domin hanyoyin ta , sai dai ta yi kira ga matuka motocin da su rinka taka tsan-tsan wajen tuki idan har an fara sayen motocin.

Hukumar kera ababen hawan ta ce za ta hada hannu da Jami'o'in kasar irin su Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, da Jami'ar Nnsuka wajen bude fanonin koyar da kere-kere musamman ma motoci domin bincike ya nuna cewa ana kashe kwatankwacin dalar Amurka biliyan 8 kowacce shekara wajen shigo da motoci daga kasashen waje.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Za A Fara Sayar Da Motocin Da Aka Kera A Najeriya Kwanan nan