Juan Guaido, wanda ya ayyana kan sa a matsayin shugaban kasa a Venezuela, ya ce za a fara wani dan kwaryakwaryan yajin aiki a yau Alhamis, wanda zai kai ga na gama gari.
Yajin aikin shi ne mataki na baya-baya da Guaido zai dauka a kokarin da yake yi na tilastawa shugaba Nicolas Maduro sauka daga kujerar shugabancin kasar ta hanyar ta da bore.
Kwanaki biyu da aka kwashe ana zanga-zanga a birnin Caracas sun janyo kazamin fada tsakanin magoya bayan Guaido da dakarun Venezuela, amma manyan sojojin kasar ba su kai ga amsa kiran da Guaido ya yi masu ba na su daina goyon bayan Maduro.
Miliyoyin ‘yan Venezuela, da suka gaji da matsalar hauhawar farashin kayayyaki da aka kasa magancewa, da matsanancin karancin abinci da man fetur, da rashin kayayyakin jinyar marasa lafiya, da kuma daukewar wutar lantarki lokuta-lokuta, sun sa mutanen tserewa daga kasar.