Wannan kuma na zuwa ne yayin da hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ke shirin fara amfani da na’urar takaita gudu wato speed meter, batun da yanzu ke cigaba da jawo cece-kuce a kasar.
Shi dai wannan sabon mataki da hukumomi ke shirin dauka a yanzu, yana daga cikin gabaren matakan rage munanan hadurra da ake yawaitar samu a kasar, kasancewar a karshen makon da ya gabata ma wani mummunan hadarin mota yayi sanadiyyar rayuka, a kusa da garin Ngurore dake jihar Adamawa, yayin da dinbin mutane cikin babbar motar dakon kaya ke komowa gida daga kasuwar garin Song.
Da yake karin haske game da wannan sabon mataki da hukumomin kare hadurra ke shirin dauka na hana hawan bel-bela, jami’in kula da sintiri da ayyukan ko ta kwana na hukumar ta Road Safety a shiyar Adamawa, Alhaji Idris Fika, ya ce daukan wannan mataki ya zama dole ganin yadda rayuka ke salwanta a kullum, sakamakon ganganci da wuce-ka-ida da direbobi ke yi musamman na manyan motoci.
Yanzu haka dai tuni jama’a suka fara maida martini game da wannan sabon matakin da hukumomin ke shirin dauka, inda wasu ke yabawa, wasu kuma ke ganin talauci ke sa wuce ka’idar.
A na su martanin, kungiyoyin direbobi a Najeriya na ganin matakin yayi dai dai. Alhaji Bello Adamu Ngurore, dake zama shugaban kungiyar direbobi ta NURTW reshen jihar Adamawa, ya ce za su bada hadin kai don kwalliya ta biya kudin sabulu.
Baya ga matsalar lalacewar hanya a Najeriya, wasu matsalolin dakan jawo munanan hadurra sun hada da tukin gangaji da kuma hawan kawarar da ake yi wa ababen hawa wanda daga baya kan jawo da-na-sani.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5