Daraktan ilimi na hukumar yaki da cin hanci a tsakanin jami’an gwamnatin Najeriya Muhammad Ashiru Baba ya ce akwai ayyukan hukumar da dama da hukumar yaki da cin hanci EFCC ke gudanarwa kuma mutane ba su fahimci hakan ba.
Ashiru Baba a zantawa da Muryar Amurka a Abuja, ya ce duk wata badakala da ta shafi jami’an gwanatin Najeriya da hakan ya hada da ‘yan siyasa, duk aikin hukumar ICPC ne.
Daraktan ya kara da cewa, aikin EFCC ya shafi sace kudi ne a fitar da su kasashen ketare da kuma ‘yan damfarar yanar gizo.
Baba ya nanata cewa hukumar ta ICPC na hukunta mutane da gurfanar da su gaban kotu kuma kwanan nan za ta fara bayyana laifuka wadanda a ke tuhuma a a bainin jama'a don su fara jin kunya tun daga duniya.
Jami’in na ICPC ya ce sun samu fahimta daga EFCC inda ta kan tura ma su duk wani bincike da ya shafi hukumar su amma ya yi batan kai ya shiga hannun EFCC.
A na sa ran bangaren, mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci EFCC Ibrahim Magu ya nanata bukata da ake yi wa kowa da ya sa hannu wajen yaki da almundahana.
Ya kara da cewa tilas ne 'yan Najeriya su bada gudummuwa idan ana son nasara, kamar yadda yake cewa, "wannan yaki ba zai yiwu mutum daya ya yi shi ba, ba kokwanto a kan hakan. Mu na bukatar hada kan 'yan Najeriya su ba mu goyon baya don haka ne mafi ingancin samun nasara".