Za a Fara Amfani Da Takardan Kudin Najeriya A Burtaniya

  • Ladan Ayawa

Kudin Naira

Daga yanzu za a rika amfani da takardar kudin Najeriya a hada-hadar kasuwancin kasar Burtaniya

Ba shakka wannan matakin ya yi wa ‘yan kasuwan Najeriya dadi kwarai da gaske.

Abu na farko dai shine wannan matakin zai rage ko ya kankare tsadar musayar kudaden ketare da Najeriya ke fuskanta musamman kudin fam da kuma dala.

Wadannan kudaden na kasashen biyu sun yi wa kudin Najeriya fintikau a kasashen duniya musamman a kasuwannin kasashen waje.

Wani masani a harkar tattalin arzikin kasa da kasa Dr Dauda Mohammed Kontagora, ya shaidawa wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin cewa wannan ba karamin tallafawa zai yi ga kudin Najeriya ba.

Yace haka zai kara tagomashi ga kudin Najeriya kuma ya samar da bunkasar tattalin arziki ga Najeriya musammam idan ace za a siyo kaya daga Najeriya.

Ga Babangida Jibrin da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Za a Fara Anfani Da Takardan Kudin Najeriya A Kasar Birtaniya 3'22