Za a fara amfani da kyamaran dake cikin wayar hannu ta salula wajan gano cutar daji da ta addabi jama’ar a sassa daban daban na duniya.
Likitocin na cigaba da zurfafa bincike da yin aiki tukuru wajen kokarin ganin cewa an maida wayar hannu wani babban abin dogaro wajan gano cututtuka kafin su habaka.
Koda yake tun farko wayar ta hannu na dauke da wasu nau’in manhajar dake tamakawa wajen auna nisan tafiya ko gudun da mutun ke yi da kuma nuna yadda zuciyar ke bugawa har ma da mai auna yawan abubuwan dake da alaka da gina jiki dake sa jikin dan Adam kara girma watau calorie.
Bada jimawa ba za a cimma burin amfani da wayar hannu ta salula wajan gano duk abubuwan dake da nasaba da kamuwa da cututtuka ciwon sukari (diabetes) ciwon daji watau (Cancer).