Jihar Florida da ke Amurka, na wani shiri na ganin an samar da dokar da za ta ba da damar amfani da jirgin sama mara matuki, “Drones” wajen yakar kananan namun daji da suka hada da macijin Mesa da ake kira a Pythons a turance.
Kwamitin Majalisar Dattawan Amurka ya amince da hukumomin jihohi biyu su yi amfani da jirage marasa matuka, a kokarin murkushe tsirrai da dabbobi.
Kudirin zai haifar da banbanci ga wata doka da ke akwai, wacce ta hana jami’an tsaro amfani da jiragen sama, domin tara bayanai tare da hana hukumomin jihohi, yin amfani da jiragen sama don tattara hotuna a kan filaye ko gidajen jama'a.
Hakan zai ba da damar Hukumar Kula da Kifi da Tsabtace Dabbobi ta jihar Florida da Ma'aikatar Kula da gandun daji, su tashi jirgin don sarrafa shi da kuma kawar da nau'in mamayar da ke faruwa a filayen jama'a.
Sen. Ben Albritton, ya ce an fada masa cewa jiragen drones din da ke dauke da manhajar da ake kira LiDAR, wacce ke iya hango alamun halittu daga nesa.
Na'urorin za su taimaka wa hukumomin wajen gano nau’ukan macizai ko kwari ‘yan asalin Asiya wadanda ke lalata ciyayi a jihar ta Florida.
Shafin yanar gizo na hukumar kula da namun daji na jihar, ya yi gargadin cewa ciyayin lygodium na yaduwa da sauri, kuma "mummunar barazana" ce ga tsibiran bishiyoyin gandun Everglades, kana hakan na kara sanya sauran gandun dazuzzuka cikin hadarin.