Za A Fara Aikin Madatsar Ruwan Mambilla Dake A Jihar Taraba

Kamfanin Sinohydro na China

Gwamnatin Najeriya na cikin shirye shiryen farfado da aikin madatsar ruwa na Mambilla dake a jihar Taraba, wanda ake sa ran idan aka kammala zai samar da Megawatt 3050 na hasken wutar lantarki, baya ga batun samar da hanyoyin noman rani ga mazauna yankin.

Aikin dai na da tarihin tafiyar hawainiya tun bayan fara batun a shekarar 1982, kusan shekaru 34 kenan. Sai dai yadda bincike ke nunawa aikin madatsar Mambillan dai an bayar da shi ne kan Dalar Amurka Biliyan Uku da Miliyan Dari Uku, kimanin Naira Biliyan Dari Biyar Da Takwas ga wani kamfanin gine gine na kasar China mai suna China Gezhouba Group Company (CGGC) da kuma kamfanin China mai suna Sinohydro.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, shine ya kaddamar da wannan aiki a shekarun baya inda yace muddin aka kammala wannan aiki to tabbas za a samu amfaninsa musamman ma ga al’umomin yankin.

Kawo yanzu dai al’ummar wannan yanki suka fara murna ga yunkurin gwamnatin shugaba Buhari ke yin a ganin an kammala aikin, Alhaji Hassan Jikan Hardo, dake zama shugaban jam’iyyar Adawa ta APC a jihar Taraba, kuma dan asalin yankin na ganin za a cika wannan alkawari da Buhari ya dauka lokacin kamfen.

To sai dai yayin da gwamnatin tarayya ke ganin kwalliya ta biya kudin sabulu ga wannan aiki na madatsar Mambilla, ita kuwa gwamnatin jihar na cewa tana na ta kokari duk kuwa da zargin da tafiyar hawainiyar da ‘yan adawa ke yi.

Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Za A Fara Aikin Madatsar Ruwan Mambilla Dake A Jihar Taraba - 3'33"