Sake gano wata wawurar da da aka yi na kudaden sayo kayan yaki, ya sa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shan alwashin fadada binciken, wanda a yanzu zai hada da nazarin ajiyar bankin wasu manyan jami’ai na farar hula da soji, wadanda aka rada irin watandar da su ka yi da kudin sayo makaman.
Shugaba Buhari ya bai wa Hukumar Yaki Da Almundahana ta (EFCC) damar binciken tsoffin manyan jami’an soji na gwamnatin irinsu tsohon Mai Bai Wa Shugaba Shawara Kan Tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Cikin karin muna-munar da aka gano har da ta sayan jiragen yaki masu saukar ungula guda biyu kan dala miliyan 136, alhalin kuwa irin wannan jirgin bai wuce dala miliyan 30 guda daya.
Tuni dai ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ke nuna goyon bayansu ga Shugaba Buhari a wannan yakin da ya ke yi da cin hanci da rashawa, a yayin da kuma ‘yan PDP ke zargin cewa bita-da-kulli ne, wasu kwararru kuma ke kiran da a shigar da batun koyar da tarbiyya a makarantu a matsayin wani bangare na yaki da cin hanci da rashawa.
Ga dai wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5