Gwamnatin ta bayyana matakin ne a cikin watan sanarwar da ma'aikatar ilimi ta fitar a yau Litinin wacce ke dauke da sa hannun daraktan yada labarai na Ma'aikatar, Ben Bem Goong.
Wannan matakin ya biyo bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa a yau tsakanin ma'aikatar ta ilimi da kwamishinonin ilimi da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi a kasar.
Sanarwar ta bayyana yadda aka umarci 'yan ajin karshe da su koma makaranta da an kammala bikin sallah mai zuwa domin shirin yin jarrabawar wacce za a fara a ranar 17 ga watan Augusta.
A tattaunawar tasu, an Kuma bayyana cewa makarantu za su bukaci taimako daga gwamnatin tarayya wajen iya budewa cikin gaggawa.
Makarantu a kasar daga matakin farko zuwa karshe sun shafe watanni a garkame saboda kokarin takaita yaduwar cutar Coronavirus.
A cikin makonnin da suka gabata gwamnatin ta bayyana cewa ba za a gudanar da jarrabawar WAEC ba saboda cutar, amma yanzu gwamnatin ta sauya matsayarta.