Za'a Bude Gasar Wasannin Motsa Jiki Na Kasa Karo Na 19

Ministan matasa da wasannin na tarayyar Najeriya Solomon Dalung, ya bayyana tabbacin cewar a yau 6 ga watan Disambar 2018, za'a bude gasar wasan motsa jiki na kasa karo na 19 (National Sport Festival).

Jihohi 35, za su samu wakilci a fadin kasar amma banda jihar Ebonyi, zasu fafata a wasannin daban daban har guda 37, wasannin na motsa jiki zai gudana ne a babban birnin tarayya dake Abuja, za'a shafe kwanaki goma kafin a karkare gasar.

Dalung yace ana sa tsammanin sama da 'yan wasa da jagorori 8,861 ne zasu halarci gasar, jimillar 'yan wasa 7,227, masu horas da 'yan wasa 710, shuwagabanin kungiyoyi su 322, akwai kuma mutane 602, wakilai daga jihohinsu wanda za'a tantancesu da zasu halarci birnin tarayyar domin gasar.

Minista Dalung ya bayyana muhimmancin bikin, wanda ya kara da cewar wasanni na kasa, da kuma na wasannin matasa na masu bautar kasa (NYSC), a matsayin babbar abun da yake kawo haɗin kai na kasa.