Masu shirya gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya a Afirka ta Kudu sun ce ba zasu haramta algaitar nan ta roba da ke kira "Vuvuzela" ba, duk da korafe-korafen da ake yi cewa su na cikawa mutane kunne.
Masu koyar da 'yan wasa, da 'yan wasan kansu da kuma masu kallon wannan gasa a telebijin, su na kukar cewa dubban irin wannan algaita da 'yan kallo ke busawa lokaci guda a yayin da ake wasa su na cika musu kunnuwa. An kamanta wannan kara ta algaitar da mamayen miliyoyin kudajen zuma.
Amma masu kare busa wannan algaitar "Vuvuzela" sun ce ai wani bangare ne na wannan gasa a Afirka ta Kudu.
Ko ta ina mutum ya leka a Afirka ta Kudu zai ga jama'a, baki da 'yan kasa, su na busa wannan algaitar roba wadda karar dubbanta ta yi kama da karar kudar zuma.