Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta tabbatar da cewar wata matashiya mai shekaru 18 ‘yar asalin kasar Saudi Arebiya, da ta gudu zuwa kasar Thailand ‘yar gudun hijira ce, inda ta bukaci kasar Australia da ta ba ta mafaka.
Ma’aikatar tsaron cikin gida ta Australia Homeland Security, ta ce za ta duba wannan bukatar ta Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya, domin ganin an samawa Rahaf Mohammd Al-Qunun mafaka.
A ranar Asabar da ta gabata ne Rahaf ta isa birnin Bangkok a wani jirgin sama da ya taso daga kasar Kuwait, bayan guduwa da ta yi daga wajen iyayenta, tana mai cewa idan ta koma za su kashe ta.
Da farko dai an hanata shiga kasar, amma bayan an kai ta Otel, ta dauki hotunan ta da wasu sakonni ta saka a shafinta na Twitter, wanda ya ja hankalin duniya, daga bisani jami’an shige-da-fice suka canza shawarar maida ta kasarta ta Saudiyya.
Shugaban jami’an shige da ficen kasar ta Thailand, ya ce mahaifin Al-Qunun da wani dan uwanta, sun isa birnin Bangkok a jiya Talata, amma ta ki amincewa ta hadu da su.