Yunkurin Koyawa Matasan Arewacin Najeriya Ilimin Harkokin Kasuwanci

Cincirindon Wasu Dalibai

Cibiyar koyan harkokin kasuwanci da ake kira Entrepreneurship Development Centre, dake shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya ta horar da wasu mutane fiye da 6000 kan koyan harkokin kasuwanci da a fannoni daban-daban musamman ma tsakanin matasa dake fama da ‘karancin ayyukan yi.

Wannan cibiya dake samun tallafin babban bankin Najeriya, ta na da ofishi a garin Maidugari bangaren da rikicin Boko Haram ya yiwa illa. Cibiyar tace tana son horas da mutane 7000 cikin ‘dan ‘kankanin lokaci don su zamo masu dogaro da kai da kuma ‘kara sanin kamomar harkokin kasuwanci.

Yanzu haka dai an yaye ‘dalibai ne daga jihohin Borno da Bauchi da Gombe da Taraba da Yobe da kuma jihar Adamawa, sai dai jihar Taraba itace ta ke da karancin ‘dalibai guda Takwas wanda ake ganin hakan bai zai rasa nasaba ba da rikice rikicen siyasa a ake fama da shi a yankin.

Shugaban cibiyar Alhaji Abubakar Abdu Gusau, ya shaidawa Muryar Amurka yadda suke horas da ‘daliban, da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen taimakwa al’umma game irin rigingimun da suka tsinci kansu ciki, har ma da ‘yan gudun hijira da yanzu haka suke cikin halin ‘ka ‘ka na kayi.

Saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Yunkurin Koyawa Matasan Arewacin Najeriya Ilimin Harkokin Kasuwanci - 4'07"