Yunkurin Hallaka Wani Dan Takarar Gwamna A Jihar Sokoto

  • Murtala Sanyinna

Sagir Attahiru Bafarawa

Lamarin ya auku ne da yammacin ranar Talata, a lokacin da wasu matasa dauke da makamai na gargajiya suka kai farmaki a gidan tsohon kwamishinan muhalli na jihar Sokoto.

A Najeriya daidai lokacin da iskar siyasa ke kara kadawa, masu son tsayawa takarar mukamai na bayyana ra'ayoyinsu, sai gashi wasu sun soma nuna fargaba akan abinda kan iya zama yunkurin hallaka su saboda siyasa.

Yanzu dai a iya cewa lamurran siyasar sun soma kankama inda tuni kuma wasu suka soma neman jam'iyusu su tsayar da su takarar mukamai daban-daban, kamar jihar Sakkwato da ke Arewa maso yammacin Najeriya, inda jam'iya mai mulki ta PDP ta ce za ta fitar da ‘yan takarar ta na mukamai ta hanyar sasantawa.

To sai ga shi daya daga cikin masu neman jam'iyar ta tsayar dasu takarar gwamna, kuma dan tsohon gwamnan jihar, Sagir Attahiru Bafarawa, ya koka akan abin da yake gani yunkurin neman ran sa.

Lamarin ya auku ne da yammacin ranar Talata, a lokacin da wasu matasa dauke da makamai na gargajiya suka kai farmaki a gidan tsohon kwamishinan muhalli na jihar Sokoto, Sagir Attahiru Bafarawa, wanda ya ajiye mukamin kwanan nan, ya kuma bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar gwamnan jihar.

“Bayan kammala sallar tarawih ne mun zo muna ganawa da mutane a nan gidana sai na shiga cikin gida. Daga can na jiwo hayaniya a waje. Ko da na fito sai aka ce wani dan ta’adda da ake kira Alu KC ne ya zo su hudu a mota, tare da babura uku kowane dauke da mutum uku” in ji Sagir Bafarawa, sa’adda yake zantawa da Muryar Amurka.

Ku Duba Wannan Ma Adalci A Zaben Fidda Gwani Kawai Zai Ba APC Nasara A Zaben Shekarar 2023 - Mambobi

Ya ci gaba da bayyana cewa “sun kutso har a harabar gidana suka zazzare takubba da adduna da wukake suna zage-zage, suna cewa ba su ji dadin da basu same ni a wajen ba, da sun aikata abin da suka zo yi.”

Duk da yake dai akwai jami’an tsaro kusa da gidan tsohon kwamishinan, to amma kuma matasan sun shammaci jama’ar da suka tattaru a harabar gidan kamar kullum, suka kutsa kai, kafin daga bisani hayaniya ta janyo hankalin jami’an tsaron wadanda nan take suka fatattaki maharan.

Gidan na Sagir Bafarawa dai na tasakiyar birnin Sokoto ne, a bayan fadar gwamnatin jihar, kuma kusa da gidan mahaifinsa, tsohon gwamnan jihar Attahiru Dalhatu Bafarawa.

Lamarin dai ya haifar da ra’ayoyi mabambanta a tsakanin jama’ar da ke unguwar, inda wasu ke zargin ko harin na da alaka da siyasa, kasancewar ya zo ne ‘yan kwanaki kalilan bayan da matashin dan shekara 38 ya ayyana kudurinsa na tsayawa takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, tare da wasu akalla mutane 4 da su ma suka yanki tikitin neman tsayawa takarar mukamin a jam’iyyar.

To sai dai Sagir Bafarawa ya ce ba zai iya tantancewa da ko lamarin na da alaka da siyasa ba ko a’a, domin kuwa shi bai san yayi sabani da kowa ba a iya saninsa.

“Ba zan iya cewa lamarin na da alaka da siyaba ba, amma dai yanzu haka jami’an tsaro sun soma aikinsu, kuma su kwararru ne da za su iya tantance ainihin dalilin wannan abu. Ina ga zai fi kyau mu ba su dama su kammala bincike kan lamarin tukunna.”

“Shi wannan Alu KC, wani gawurtaccen ‘Area Boy’ ne a nan Sokoto, kuma kowa ya san shi. Yanzu haka ma jami’an tsaro sun ce suna cikin nemansa bisa zarge-zargen kisan kai har 3 da ake yi masa” a cewar Bafarawa.

Ku Duba Wannan Ma Gwamnoni A Najeriya Na Kara Juya Akalar Siyasar 2023

Kawo lokacin wallafa wannan labari, babu rahoton kama wadanda ake zargi da kai harin, amma dai an kai rahoton ga hukumar ‘yan sanda, wadda kuma aka ce tuni da ta soma neman wadanda ake zargi da kai farmakin.

To sai dai duk yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar bai yi nasara ba, domin kuwa bai dauki dimbin kiraye-kirayen wayar tarho da aka yi masa ba, haka kuma bai amsa sakon kar-ta-kwana da aka aika masa ba.

Jihar Sokoto dai ta yi kaurin suna kan ‘yan bangar siyasa a shekarun da suka gabata musamman a irin wannan lokaci da aka soma kada gangar siyasa, to amma lamarin ya dan yi sauki a ‘yan shekarun nan.

Sai dai kuma jama’a na cikin fargabar yiwuwar dawowar rikice-rikicen, wadanda aka soma gani sare-sarinsu a kwaryar birnin Sokoto, wadanda kuma galibi sukan soma tun daga wurin lika hotunan ‘yan takara.

Saurari cikakkiyar zantawa da Sagir Bafarawa kan harin da aka ki a gidansa.

Your browser doesn’t support HTML5

Yunkurin Hallaka Wani Dan Takarar Gwamnan Jihar Sokoto