Yunkurin Halatta Tabar Wiwi a Najeriya

Tabar Wiwi

Dokar halitta tabar wiwi dake jiran a bude mata dandalin sauraren ba'asin jama'a ta hada da wasu sharuda kamar yadda Madam Mirian Onuoha, yar Majalisar Wakilai daga Jihar Imo wadda ta samar da dokar ta bayyana.

Mirian ta ce tana son dokar ta daidaita yadda za yi noman tabar wiwi da yadda za a mallake ta, da kuma kasuwancinta ta yadda gwamnati za ta samu kudin shiga, baya ga haka tana son ayi amfani da ita ta hanyar neman lafiya.

Madam Mirian Onuoha, ta ce dole ne mai nomawa da sayar da tabar wiwi ya samu lasisi daga hannun gwamnati, ta yadda in ya kauce wa ka'ida wajen sayarwa, shi da mai saye suna iya fuskantan barazanar dauri a gidan gyara hali har na shekaru biyu ko kuma ya biya tara har ta Naira 500,000.

To saidai wanan doka ta dauki hankalin kwararrun likitoci da manyan wasu malaman addinai wadanda suka baiyana ra'ayin su agame da wanan doka.

Kwararren likita mai zaman kansa Dokta Abu Yazid, ya nuna damuwa akan yadda yan Majalisu ke halatta abubuwa, inda ya ce an halatta shan giya da shan kwayoyi da taba, yanzu kuma tabar wiwi ake so a halatta.

Dokta Abu Yazid ya ce dukan abubuwan da ya lissafa suna da illa a jikin dan Adam, kuma in ta hanyar samun kudin shiga ne, akwai hanyoyi da dama da ya kamata a samu kudi da su kuma gwamnati tana iya kokarin ta.

Shi ma babban Limamin Kirista James Movel Wuye, na cibiyar wanzar da zaman lafiya a tsakanin addinai, ya ce in har an ce za a kaiyade tabar wiwi domin neman magani to dole a yi amfani da hukumar sarrafa magunguna ta kasa, idan za su yi haka su yi hattara, a yi sara ana duba bakin gatari, kan ko zai iya tamakawa mutane to zai taimaka wa mutane amma abu ne da ya kamata a yi taka tsantsan wajen kafa irin wannan dokar.

A lokacin da yake nashi nazarin shugaban kungiyar JIBWIS ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce wannan doka ba ta da wani amfani a kasa, saboda haka yana kira da a yi fatali da ita.

Shi ma shugaban hukumar kula da fataucin miyagun kwayoyi Janar Buba Marwa, ya fitar da wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bashi shawara a harkar hulda da manema labarai Femi Babafemi, inda ya ce a ya nazari mai zurfi kafin a yi irin wannan dokar.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Yunkurin Halatta Tabar Wiwi a Najeriya - 2'44"