Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar kasar Morocco Youssef En-Nesyri ya koma kungiyar Sevilla da taka leda.
Youssef mai shekara 22 da haihuwa, ya amince ya sanya hannu akan yarjejeniyar shekara biyar, inda zai kammala a shekarar 2025.
A yau Alhamis 16 ga watan Janairun 2020 kungiyar ta Sevilla, ta sanar da sayen dan wasan, akan kudi euro miliyan €20m kwatankwacin dalar Amurka miliyan $22.3.
Youssef ya buga wasa a kungiyar Leganes, bayan ya bar Malaga, a shekarar 2018, ya zira kwallaye 15, cikin wasanni 53, da ya buga inda ya zamo dan wasan da ya fi kowa jefa kwallaye a kungiyar.
Bayan haka dan wasan ya kasance a cikin tawagar 'yan wasan kasar Morocco, a gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka, da kuma gasar cin kofin duniya na 2018.
Sevilla ta dauko dan wasan ne bayan ta rabu da nata dan wasan mai suna Munas Dabbur, wanda ya koma Hoffenheim a wannan watan.