Bamabaman sun yi sanadiyar mutuwar mutane shida da kuma raunata wasu ashirin da shida.
Bamabaman din sun tashi ne a wurare daban daban. Bom na farko ya tashi ne a bakin tasha inda wata 'yar kunar bakin wake tayi kokarin kutsawa cikin jama'a kafin bom din ya tashi da ita ya hallakata da wasu mutane hudu.
Bom na biyu ya tashi ne da wani saurayi da aka ce ya fito ne daga daji kana yayi kokarin shiga kekenapep samfarin baburan nan masu kafofi uku inda matukin keken ya gano cewa dan saurayin na dauke da bom. Saurayin ya tada bom din saidai shi kadai ya gamu da ajalinsa.Dan saurayin bai wuce shekaru goma sha uku da haihuwa ba.
Mai magana da yawun gwamnatin jihar Yobe yace an samu bala'i a babban birnin jihar inda bamabamai suka tashi da suka yi sanadiyar mutuwar mutane shida da suka hada da 'yan kunar bakin waken..
Cikin mutane 26 da suka raunata hudu sun yi muni har an shigar da su dakin tiyata saboda a y i masu aiki. Gwamnatin jihar ta dauki alkawarin biyan kudin jinyarsu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5