Jihar Yobe ta nemi afuwa dangane da sanarwar da ta yi kan ceto 'yan matan da suka bace daga makarantar sakandaren mata ta garin Dapchi da ke Jihar bayan da 'yan Boko Haram suka kai hari a makarantar da daren Litinin.
Jihar ta bayyana cewa ta dogara ne da bayanan da daya daga cikin hukumomin tsaron da ke yaki da Boko Haram, wanda hakan ya sa suka ga ba wata shakka a ciki.
Sai dai yanzu ta gane cewa babu sahihanci tare da bayanan a saboda haka ta ke neman afuwa.
Gwamnan Jihar, Ibrahim Gaidam ya ziyarci Dapchi a yau inda ya gana da shugabannin al'ummar garin,da shugaban makarantar da ma'aikatanta. Inda ya gana da wasu daga cikin iyayen 'yan matan da suka koka kan cewa har yanzu ba su ga 'ya'yansu ba.
Gwamnan ya bukaci Jami'an ma'aikatar ilimi da na makarantar Dapchi da su yi aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da an gane iya adadin wadanda suka bace da sauran bincike.
A jiya dai Gwamnatin jihar ta bayyana cewa daga cikin 'yan makarantar 926, guda 50 ne suka bace amma wasu rahotanni na nuni da cewa adadin ya wuce hakan.