YOBE: An Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Domin Tallafawa ‘Yan Gudun Hijira

A jiya ne gwamnatin jihar Yobe ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki na yini guda game da samar da agaji ga wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, da kuma sake farfado da garuruwan da ‘yan boko haram din suka lalata bayan kwato su da rundunar sojin Najeriya ta yi.

Wadannan ne batutuwan da aka sa gaba a wannan taro, kuma masana da hukumomin agaji sun gabatar da kasidu daban daban game da matsalolin da ake fuskanta, da kuma hanyoyin da za a bi domin magance irin wadannan matsaloli a nan gaba.

Yayin da yake bude taron, gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam, ya ce kodashike yanzu an ci karfin ‘yan kungiyar, yanzu abin da za a sag aba shine yadda za a sake tsugunar da jama’ar da rikicin ya dai daita.

“ya ce kamar yadda kuka sani, gwamnatin jihar Yobe, ta soma ayyukan gyaran garuruwan da ‘yan kungiyar boko haram suka lalata, da kluma tallafawa wadanda iftila’in ya shafa, wanda yawancinsu sun koma garuruwansu na asali.”

Ya kara da cewa yanzu haka jihar tana da ‘yan gudun hijira kasa da dubu biyu ne kawai da aka san zaman su a sansanin ‘yan gudun hijira, kuma a yanzu haka ma da dama na shirye shiryen komawa garuruwansu.

Domin Karin bayani ga cikakken rahoton Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

YOBE: An Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Domin Tallafawa ‘Yan Gudun Hijira