Yayin Da Turai Ke Bude Kofofinta, China Na Sake Kakkaba Matakai

Wasu ma'aikata kenan lokacin da suke cire wata katanga yayin da ake ci gaba da sassauta dokokin takaita zirga-zirga a kasar Italiya.

Ana ci gaba da bude wuraren da aka rurrufe a Faransa da Birtaniya da Girka, yayin da kasar China ke sake kakaba wasu sabbin matakan coronavirus, bayan samun sabbin wadanda su ka kamu da cutar a Beijing.

Masu gidajen abinci a birnin Paris za su iya bude kokofinsu kamar na sauran takwarorinsu a fadin kasar, ta hanyar barin kwastomomi su zauna su ci abinci a ciki.

Matafiya daga sauran kasashen Turai suma za su iya zuwa Faransa a daidai lokacin da kasar ta bude kofarta ga matafiyan yankin.

“Dole mu sake kaddamar da tattalin arzikinmu,” a cewar shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.

A Birtaniya, shagunan da ayukansu ba masu muhimmanci bane su ma za su iya budewa daga yau Litinin, a wuraren bauta da kuma wuraren shakatawa da su ka hada da wajen kallon fina-finai da ake kallo daga mota da kuma gidajen namun daji.

Mutane zasu ci gaba da baiwa juna tazara, kuma gwamnati tana bayar da shawarar a ci gaba da amfani da takunkumin fuska lokacin da mutane suka hadu.