Wakilin kwararren ‘dan wasan nan Yaya Toure mai suna Dimitri Seluk yayi da’awar cewa ‘dan wasan zai bar kungiyar Manchester City bayan wannan kakar wasan bana.
Yaya Toure dai yanada sauran shekaru biyu a kwantaraginsa na yanzu da ake biyan sa yiro dubu dari biyu a sati, har an shirya cewa zai gamu da shugaban kungiyar Manchester City a karshen wasannin da ake.
Ana ganin dai za’a baiwa Toure damar barin kungiyar, kamar yadda tsohon zakaran gasar kalubalen kwararru ta Champion League zai fara gina kungiyar sa kafin zagayowar kakar wasa mai zuwa.
Koch ‘din kungiyar Inter Millan Roberto Mancini na matukar son ya dawo da Yaya Toure zuwa kungiyar sa, bayan da yake ikirarin cewa “‘dan shekaru 32 kamar ‘da ne a gareshi.”
Dimitri Suluk dai yace yana da tabbacin cewa Yaya Toure zai bar kungiyar Manchester City bayan kakar wasan bana, alokacin da yake magana da mujallar wassanni ta sky sport news.
Ya kuma kara da cewa har yanzu dai ba’a kai ga matsaya ba, muna dai jira har sai karshen kakar wasan bana.